Karin Magana 24:3
Ana nuna aya 3 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
2
gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.
3
Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
4
ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.
5
Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
6
don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.
Settings