Hikima Tana Kariya Daga Mugayen Mutane
12
Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
13
waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
14
waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
15
waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
Settings