Karin Magana 1:10-16
10
Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
11
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
12
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
15
ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16
gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.
Settings