Skip to content
Ƙidaya 8:16-26

Ƙidaya 8:16-26

16
Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.
17
Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.
18
Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila.
19
Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”
20
Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa.
21
Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su.
22
Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
23
Ubangiji ya ce wa Musa,
24
“Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada,
25
amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki.
26
Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options