Ƙidaya 8:1-15
1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ”
3
Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
4
Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa.
5
Ubangiji ya ce wa Musa,
6
“Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.
7
Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu.
8
Ka sa su ɗauki ɗan bijimi tare da lallausan garin hadaya, kwaɓaɓɓe da mai; sa’an nan, kai kuma ka ɗauki ɗan bijimi na biyu na hadaya don zunubi.
9
Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka.
10
Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu.
11
Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji.
12
“Bayan Lawiyawa sun ɗibiya hannuwansu a kan bijiman, sai ka yi amfani da ɗaya a matsayin hadaya don zunubi ga Ubangiji, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa, don yin kafara saboda Lawiyawa.
13
Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da ’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.
14
Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa.
15
“Bayan ka tsarkake Lawiyawa, ka kuma miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, sai su zo su yi aikinsu a Tentin Sujada.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings