Ƙidaya 35:19-29
19
Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi.
20
In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu,
21
ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi.
22
“ ‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba,
23
ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba,
24
dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi.
25
Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.
26
“ ‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je,
27
idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba.
28
Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa.
29
“ ‘Waɗannan su ne za su zama ƙa’idodin da za ku kasance da su, a dukan tsararraki masu zuwa.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings