Ƙidaya 3:1-19
1
Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa a lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai.
2
Sunayen ’ya’yan Haruna su ne, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Eleyazar da Itamar.
3
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Haruna, shafaffun firistocin da aka naɗa domin su yi aiki firist.
4
Amma Nadab da Abihu suka fāɗi suka mutu a gaban Ubangiji a Hamadar Sinai a sa’ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta a gabansa. Ba su kuwa da ’ya’ya; saboda haka Eleyazar da Itamar kaɗai suka yi aiki firist a zamanin mahaifinsu Haruna.
5
Ubangiji ya ce wa Musa,
6
“Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki.
7
Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul.
8
Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul.
9
Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da ’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi.
10
Ka naɗa Haruna da ’ya’yansa su yi aiki firistoci; duk wanda ya yi shisshigi a wuri mai tsarki kuwa dole a kashe shi.”
11
Ubangiji ya kuma ce wa Musa,
12
“Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne,
13
gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”
14
Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai ya ce,
15
“Ka ƙidaya Lawiyawa bisa ga iyalansu da kabilarsu. Ka ƙidaya kowane ɗan jinjiri mai wata ɗaya ko fiye.”
16
Saboda haka Musa ya ƙidaya su duka, kamar yadda maganar Ubangiji ta umarta.
17
Ga sunayen ’ya’yan Lawi, Gershon, Kohat da Merari.
18
Ga sunayen mutanen Gershon, Libni, da Shimeyi
19
Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
Settings