Ƙidaya 29:1-11
1
“ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni.
2
Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani.
3
Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;
4
kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
5
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.
6
Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi.
7
“ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba.
8
Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma ’yan raguna bakwai, ’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
9
Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai;
10
kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
11
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.
Settings