Skip to content
Ƙidaya 28:5-15

Ƙidaya 28:5-15

5
tare da hadaya ta lallausan gari kashi ɗaya bisa goma na efan, kwaɓaɓɓe da kwalaba ɗaya na man zaitun mafi kyau.
6
Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kullum wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
7
Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.
8
Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa shi da yamma, tare irin hadaya ta lallausan gari, da hadaya ta sha da ka yi da safe. Wannan hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
9
“ ‘A ranar Asabbaci, za a miƙa ’yan raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya marasa lahani, tare da hadaya ta sha, da hadaya ta lallausan gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai.
10
Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha.
11
“ ‘A rana ta fari ga kowane wata, za a miƙa wa Ubangiji hadayun ’yan bijimai biyu, rago ɗaya, da ’yan tumaki bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu kuma marasa lahani.
12
Da kowane bijimi, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi uku bisa goma na efa; da ɗan rago kuwa, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai na kashi biyu bisa goma na efa;
13
da kowane tunkiya kuma, a kasance da hadaya ta lallausan garin da aka kwaɓa da mai, na kashi ɗaya bisa goma na efa. Wannan hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
14
Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara.
15
Ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadaya ta sha, za a miƙa bunsuru ɗaya ga Ubangiji, hadaya ce don zunubi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options