Ƙidaya 26:29-34
29
Zuriyar Manasse, daga Makir, kabilar Makiriyawa (Makir shi ne mahaifin Gileyad); daga Gileyad, kabilar Gileyadawa.
30
Waɗannan su ne zuriya Gileyad, daga Iyezer, kabilar Iyezerawa; daga Helek, kabilar Helekawa;
31
daga Asriyel, kabilar Asriyelawa; daga Shekem, kabilar Shekem;
32
daga Shemida, kabilar Shemadawa; daga Hefer, kabilar Heferawa.
33
(Zelofehad ɗan Hefer, ba shi da ’ya’ya maza; ’yan mata ne kaɗai ya haifa, sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.)
34
Waɗannan su ne kabilan Manasse, jimillarsu ta kai 52,700.
Settings