Skip to content
Ƙidaya 23:13-24

Ƙidaya 23:13-24

13
Sa’an nan Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su; a nan kana ganin sashe ne kawai, ba dukansu ba. Daga can kuwa, ka la’anta mini su.”
14
Saboda haka ya ɗauke shi zuwa filin Zofim a ƙwanƙolin Fisga, a can ya gina bagadai bakwai, ya kuma miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
15
Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in je in sadu da Ubangiji a can.”
16
Ubangiji ya sadu da Bala’am, ya kuma ba shi saƙo ya ce, “Koma wurin Balak ka ba shi wannan saƙo.”
17
Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?”
18
Sai Bala’am ya furta saƙon da aka ba shi ya ce, “Tashi, Balak, ka saurara; ka kasa kunne gare ni, ɗan Ziffor.
19
Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
20
Na karɓi umarni in sa albarka; na kuwa sa albarka, ba zan iya janye ta ba.
21
“Bai ga mugunta a cikin Yaƙub ba, bai kuma ga wahala a Isra’ila ba. Ubangiji Allahnsu yana tare da su; sowar Sarki yana cikinsu.
22
Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfi iri na kutunkun ɓauna.
23
Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub, ba sihiri da zai cuci Isra’ila. Yanzu za a ce game da Yaƙub da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!’
24
Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya; sun tā da kansu kamar zaki wanda ba ya hutawa sai ya cinye naman abin da ya kama ya kuma sha jinin abin da ya kama.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options