Ƙidaya 19:17-21
17
“Ga wanda ya ƙazantu kuwa, a ɗiba toka daga hadaya ta ƙonawa ta tsarkakewa, a zuba a cikin tulu, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu a kansu.
18
Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah.
19
A rana ta uku, da ta bakwai kuma mai tsarkakewa zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, a rana ta bakwai kuma yă tsarkake shi. Wanda aka tsarkaken kuwa, dole yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka da yamma, zai kuma tsarkaka.
20
Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta.
21
Wannan za tă zama musu dawwammamiyar farilla. “Mutumin da ya yayyafa ruwa na tsarkakewa, shi ma dole yă wanke rigarsa. Duk wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa, zai kasance da ƙazanta har yamma.
Settings