Ƙidaya 15:12-16
12
Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.
13
“ ‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
14
Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.
15
Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.
16
Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’ ”
Settings