Ƙidaya 1:49-53
49
“Ka tabbatar ba ka ƙidaya mutanen Lawi ko kuma ka haɗe su tare a ƙidayan sauran Isra’ilawa ba.
50
A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi.
51
Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.
52
Sauran Isra’ilawa za su zauna ƙungiya-ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa daidai bisa ga ƙa’idarsa.
53
Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”
Settings