Skip to content
Nehemiya 6:17-19

Nehemiya 6:17-19

17
A waɗannan kwanaki, manyan garin Yahuda suka yi ta aika wasiƙu masu yawa zuwa ga Tobiya, shi kuma ya yi ta aika musu da amsoshi.
18
Gama mutane da yawa a cikin Yahuda sun rantse wa Tobiya za su goyi bayansa, domin ya auri ’yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato, Yehohanan, ya auri ’yar Meshullam, ɗan Berekiya.
19
Ban da haka ma, mutanen sun yi ta ba ni labarin ayyuka masu kyau da Tobiya ya yi, sa’an nan kuma suna faɗa masa duk abin da na faɗa. Tobiya kuwa ya aika wasiƙu don yă tsorata ni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options