Nehemiya 13:1-3
1
A wannan rana aka karanta Littafin Musa da ƙarfi a kunnuwan mutane aka kuma sami an rubuta cewa kada a karɓi mutumin Ammon ko mutumin Mowab cikin taron Allah,
2
domin ba su taryi Isra’ila da abinci da ruwa ba amma suka yi hayar Bala’am don yă kira la’ana a kansu. (Amma Allahnmu, ya mai da la’anar ta zama albarka.)
3
Sa’ad da mutane suka ji wannan doka, sai suka ware daga Isra’ila duk waɗanda suke na baƙon zuriya.
Settings