Nehemiya 12:45-47
45
Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon.
46
Gama tun dā, a kwanakin Dawuda da Asaf, akwai masu bi da mawaƙa da kuma na waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.
47
Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna.
Settings