Nehemiya 10:30
Ana nuna aya 30 tare da mahallin da ke kewaye.
27
da Malluk, da Harim da kuma Ba’ana.
28
“Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan ’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta,
29
dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari ’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba.
30
“Mun yi alkawari ba za mu ba da ’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanmu maza ba.
31
“Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi.
32
“Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu.
33
Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu.
Settings