Nahum 3:12-19
12
Dukan kagarunki suna kama da itatuwan ɓaure da ’ya’yansu da suka nuna. Da an girgiza, sai ɓaure su zuba a bakin mai sha.
13
Dubi mayaƙanki, duk mata ne! Ƙofofin ƙasarki a buɗe suke ga abokan gābanki, wuta ta cinye madogaransu.
14
Ki ja ruwa gama za a kewaye ki da yaƙi. Ki ƙara ƙarfin kagaranki! Ki kwaɓa laka, ki sassaƙa turmi ki gyara abin yin tubali!
15
A can wuta za tă cinye ki; takobi zai sare ki, kuma kamar fāra, za a cinye ki. Ki riɓaɓɓanya kamar fāra, ki riɓaɓɓanya kamar fārin ɗango!
16
Kin ƙara yawan masu kasuwancinki har sai da suka fi taurarin sama. Amma kamar fāra sun cinye ƙasar sa’an nan suka tashi, suka tafi.
17
Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango, shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi, amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi, ba kuma wanda ya san inda suka nufa.
18
Ya sarkin Assuriya, makiyayanka sun yi barci; manyan mutanenka sun kwanta su huta. An watsar da mutanenka a cikin duwatsu, ba wanda zai tattaro su.
19
Ba abin da zai warkar da rauninka; rauninka ya yi muni. Duk wanda ya ji labarinka zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka, gama wane ne bai ji jiki a hannunka ba?
Settings