Mika 1:5-7
5
Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?
6
“Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
7
Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”
Settings