Mattiyu 25:1-8
1
“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.
2
Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.
3
Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.
4
Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.
5
Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.
6
“Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’
7
“Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.
8
Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’
Settings