Mattiyu 15:29-31
29
Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna.
30
Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su.
31
Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.
Settings