Mattiyu 12:23
Ana nuna aya 23 tare da mahallin da ke kewaye.
20
Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
21
Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
22
Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
23
Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”
24
Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”
25
Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.
26
In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?
Settings