Skip to content
Markus 8:14-21

Markus 8:14-21

14
Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan.
15
Yesu ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”
16
Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”
17
Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?
18
Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba?
19
Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka amsa, “Sha biyu.”
20
“Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka ce, “Bakwai.”
21
Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options