Skip to content
Markus 5:17-24

Markus 5:17-24

17
Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu.
18
Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi.
19
Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”
20
Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
21
Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin.
22
Sai ɗaya a cikin masu mulkin majami’a, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa,
23
ya roƙe shi da gaske ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.”
24
Sai Yesu ya tafi tare da shi. Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options