Luka 9:46-50
46
Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma
47
Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.
48
Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”
49
Sai Yohanna ya ce, “Ubangiji, mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka yi ƙoƙarin hana shi, don shi ba ɗaya ba ne daga cikinmu.”
50
Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”
Settings