Skip to content
Luka 6:37-42

Luka 6:37-42

37
“Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.
38
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”
39
Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?
40
Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.
41
“Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba?
42
Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options