Luka 6:39-45
39
Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?
40
Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.
41
“Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba?
42
Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.”
43
“Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
44
Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya.
45
Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”
Settings