Skip to content
Luka 17:7-10

Luka 17:7-10

7
“In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba’?
8
Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba’?
9
Shin, zai gode wa bawan don yă yi aikin da aka ce ya yi ne?
10
Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options