Skip to content
Firistoci 8:14-23

Firistoci 8:14-23

14
Sa’an nan ya miƙa bijimi domin hadaya don zunubi, sai Haruna da ’ya’yansa suka ɗibiya hannuwansu a bijimin.
15
Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa.
16
Musa ya ɗebo dukan kitsen da yake kewaye da kayan ciki, da kuma wanda ya rufe hanta, da ƙodojin, da kuma kitsensu, ya kuma ƙone su a kan bagade.
17
Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi.
18
Sa’an nan ya miƙa ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan rago.
19
Sa’an nan Musa ya yanka ɗan ragon, ya kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagaden.
20
Ya yanka ragon gunduwa-gunduwa ya ƙone kan, ya kuma ƙone gunduwa-gunduwan da kitsen.
21
Ya wanke kayan cikin da ƙafafun a ruwa, ya kuma ƙone dukan ragon a bisa bagade kamar hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
22
Sai ya miƙa ɗayan ɗan ragon, ɗan ragon naɗin, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan ragon.
23
Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options