Firistoci 6:7
Ana nuna aya 7 tare da mahallin da ke kewaye.
4
sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.
5
Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.
6
A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa.
7
Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.”
8
Ubangiji ya ce wa Musa,
9
“Ka ba Haruna da ’ya’yansa maza wannan umarni, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za tă kasance a bagade dukan dare, sai da safe, kuma dole a bar wutar tă yi ta ci a bisa bagaden.
10
Sa’an nan firist zai sa rigunarsa ta lilin da kuma rigar lilin da ake sa a ciki, sa’an nan yă kwashe tokan hadaya ta ƙonawa da wuta da ta ci a kan bagaden, yă sa kusa da bagaden.
Settings