Firistoci 25:47-50
47
“ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon,
48
yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa.
49
Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa.
50
Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.
Settings