Firistoci 25:1-6
1
Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce,
2
“Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji.
3
Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu.
4
Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi.
5
Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.
6
Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba,
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings