Skip to content
Firistoci 15:25-30

Firistoci 15:25-30

25
“ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta.
26
Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta.
27
Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.
28
“ ‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki.
29
A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada.
30
Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options