Skip to content
Firistoci 14:38-45

Firistoci 14:38-45

38
firist ɗin zai fita a bakin ƙofar gidan ya rufe ta na kwana bakwai.
39
A rana ta bakwai ɗin firist zai dawo don yă dudduba gidan. In cutar fatar jiki da take a riga ta yaɗu a bangayen,
40
zai umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar a zubar a wuri marar tsarki waje da birnin.
41
Dole yă sa a kankare duka shafen bangon cikin gidan a kuma zuba kayan da aka kankare a wurin marar tsarki waje da birnin.
42
Sai su ɗebi waɗansu duwatsu su sa a wuraren da suka ciccire waɗancan, su kuma ɗiba sabon laka su yi shafen gidan.
43
“In cutar fatar jiki da take ta rigar ta sāke bayyana a gidan bayan an ciccire duwatsu aka kankare gidan aka kuma yi shafe,
44
firist zai je ya bincika shi, in kuwa cutar ta bazu a gidan, to, muguwar cuta ce; gidan marar tsarki ne.
45
Dole a rushe gidan, a fid da duwatsun, katakai da kuma dukan shafen daga birnin zuwa wuri marar tsarki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options