Skip to content
Firistoci 13:9-17

Firistoci 13:9-17

9
“Sa’ad da wani yana da cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga firist.
10
Firist zai bincike shi, in kuwa farin kumburi a fatar jikin ya juyar da gashin fari in kuma akwai sabon miki a kumburi,
11
to, cutar fatar jikin ne mai ƙarfi kuma firist zai furta shi marar tsarki. Ba zai kaɗaice shi ba, domin ya riga ya zama marar tsarki.
12
“In cutar ta fashe ko’ina a fatar jiki, har iyakar ganin firist, ta rufe dukan fatar jikin mai fama da cutar, daga kai har zuwa ƙafa,
13
firist zai bincike shi, in cutar ta riga ta rufe dukan jikinsa, zai furta wannan mutum tsarkakakke ne. Da yake ya juya fari fat, tsarkakakke ne.
14
Amma sa’ad da sabon miki ya bayyana a jikinsa, zai furta shi marar tsarki.
15
Sa’ad da firist ɗin ya ga sabon miki, zai furta shi marar tsarki. Sabon mikin marar tsarki, yana da cuta mai yaɗuwa.
16
A ce sabon mikin ya canja ya juya fari, dole yă je wurin firist.
17
Firist zai bincike shi, in kuma mikin ya juya ya zama fari, firist zai furta mai cutar tsarkakakke; to, zai zama tsarkakakke.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options