Mahukunta 9:8-15
8
Wata rana itatuwa suka fita don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Ka zama sarkinmu.’
9
“Amma itacen zaitun ya ce, ‘In bar mai nawa, wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in zo in yi ta fama da itatuwa?’
10
“Biye da wannan, sai itatuwan suka ce wa itacen ɓaure, ‘Zo ka zama sarkinmu.’
11
“Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan ’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’
12
“Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’
13
“Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’
14
“A ƙarshe sai dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo ka zama sarkinmu.’
15
“Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’
Settings