Mahukunta 5:6-11
6
“A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, an yashe dukan hanyoyi; matafiye suka bi hanyoyin da suka yi kona-kona.
7
Rayuwar ƙauye a Isra’ila ta daina, ta daina sai da ni, Debora, na taso, na taso mahaifiya a Isra’ila.
8
Sa’ad da suka zaɓi sababbin alloli, sai ga yaƙi a ƙofofin birnin, ba a kuwa ga garkuwa ko māshi a cikin mutum dubu arba’in a Isra’ila ba.
9
Zuciyata tana tare da ’ya’yan sarakunan Isra’ila, tare da masu niyyar ba da kansu da yardan rai cikin mutane. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
10
“Ku da kuke hawan fararen jakuna, kuna zama a sirdin barguna, da ku da kuke tafiya a kan hanya, ku kula
11
da muryoyin mawaƙa a wuraren ruwaye. Suna faɗi ayyukan adalcin Ubangiji, ayyukan adalcin mayaƙansa a Isra’ila. “Sa’an nan mutanen Ubangiji suka gangara zuwa ƙofofin birni.
Settings