Mahukunta 3:12
Ana nuna aya 12 tare da mahallin da ke kewaye.
9
Amma da suka yi kuka ga Ubangiji, sai ya tad musu da mai ceto, Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb wanda ya cece su.
10
Ruhun Ubangiji ya sauko masa, domin yă zama mahukuncin Isra’ila yă kuma je yaƙi. Ubangiji ya bayar da Kushan-Rishatayim sarkin Aram a hannun Otniyel, ya kuwa sha ƙarfinsa.
11
Saboda haka ƙasar ta zauna da lafiya shekara arba’in har sai da Otniyel ɗan Kenaz ya rasu.
12
Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila.
13
Da ya sami Ammonawa da Amalekawa suka haɗa hannu tare, sai Eglon ya tafi ya auka wa Isra’ila, suka ƙwace Birnin Dabino.
14
Isra’ilawa suka zama bayin Eglon sarkin Mowab shekara goma sha takwas.
15
Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab.
Settings