Skip to content
Yoshuwa 9:7-15

Yoshuwa 9:7-15

7
Mutanen Isra’ila kuwa suka ce wa Hiwiyawa, “Wataƙila kuna kusa da mu, ta yaya za mu yi alkawari da ku?”
8
Suka ce wa Yoshuwa, “Mu bayinku ne.” Amma Yoshuwa ya tambaye su ya ce, “Ku wane ne, kuma daga ina kuka zo?”
9
Suka amsa suka ce, “Bayinka sun zo ne daga ƙasa mai nisa gama Ubangiji Allahnka ya yi suna sosai. Gama mun ji labarin abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ya yi a Masar
10
da kuma duk abubuwan da ya yi wa sarakuna biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot.
11
Dattawanmu da duk mazaunan ƙasar, suka ce mana, ‘Ku ɗauki abincin tafiyar da za ku riƙe; ku je ku same su ku ce musu, “Mu bayinku ne, ku yi alkawari da mu.” ’
12
Abincin tafiyan nan namu yana da ɗumi lokacin da muka kintsa tashi daga gida a ranar da za mu kama hanya zuwa wurinku. Amma yanzu duba yadda ya bushe, ya yi fumfuna.
13
Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.”
14
Mutanen Isra’ila suka ɗiba daga cikin abincin tafiyar amma ba su nemi nufin Ubangiji ba.
15
Sa’an nan Yoshuwa ya yi alkawari zaman salama da su, cewa ba zai kashe su ba, sai shugabannin mutanen Isra’ila kuwa suka tabbatar musu da haka ta wurin yin rantsuwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options