Skip to content
Yoshuwa 7:13-16

Yoshuwa 7:13-16

13
“Tashi, ka je ka tsarkake mutane. Ka ce musu su tsarkake kansu, su yi shiri domin gobe; gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, a cikinku akwai abubuwan da aka keɓe, ya Isra’ilawa. Ba za ku iya yin tsayayya da abokan gābanku ba sai in kun rabu da abubuwan nan da aka haramta.
14
“ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum.
15
Mutumin da aka same shi da haramtattun abubuwan kuwa za a ƙone shi, duk da mallakarsa domin ya karya sharaɗin da Ubangiji ya yi muku, ya yi abin kunya a Isra’ila!’ ”
16
Kashegari da sassafe Yoshuwa ya sa Isra’ilawa suka fito kabila-kabila, aka ware kabilar Yahuda.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options