Skip to content
Yoshuwa 2:12-18

Yoshuwa 2:12-18

12
Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa
13
za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”
14
Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”
15
Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.
16
Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”
17
Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba
18
sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options