Skip to content
Yoshuwa 18:1

Yoshuwa 18:1

Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Isra’ilawa duka suka taru a Shilo suka kafa tenti inda za su dinga taruwa. Yanzu ƙasar tana ƙarƙashin mulkinsu,
2
amma akwai sauran kabilu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su samu rabon gādonsu ba tukuna.
3
Saboda haka Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na iyayenku ya ba ku?
4
Ku ba da mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su zagaya dukan ƙasar su rubuta bayani game da ita, bisa ga yadda za a raba ta gādo ga kowace kabila, sa’an nan su dawo wurina.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 90 chars

Options