Yoshuwa 14:12-15
12
Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa.”
13
Sai Yoshuwa ya sa wa Kaleb ɗan Yefunne albarka, ya ba shi Hebron.
14
Saboda haka Hebron ta zama ƙasar Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze tun daga lokacin nan, domin ya bi Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa.
15
(Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.
Settings