Yohanna 9:13-17
13
Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa.
14
To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce.
15
Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.”
16
Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban.
17
A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”
Settings