Yohanna 5:31-47
31
“In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce.
32
Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce.
33
“Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya.
34
Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto.
35
Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
36
“Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni.
37
Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba,
38
maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba.
39
Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina,
40
duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
41
“Ni ba na neman yabon mutane,
42
na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku.
43
Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.
44
Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
45
“Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.
46
Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.
47
Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
Settings