Yohanna 19:17-20
17
Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota).
18
Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
19
Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.
20
Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik.
Settings