Yohanna 11:47-52
47
Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
48
In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
49
Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!
50
Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
51
Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,
52
ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.
Settings