Skip to content
Yohanna 11:17-37

Yohanna 11:17-37

17
Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari.
18
Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima,
19
Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu.
20
Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
21
Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.
22
Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
23
Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.”
24
Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
25
Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;
26
kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”
27
Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
28
Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.”
29
Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa.
30
Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi.
31
Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
32
Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
33
Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu.
34
Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
35
Yesu ya yi kuka.
36
Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37
Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options