Ayuba 42:2-6
2
“Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa; ba wanda zai iya ɓata shirinka.
3
Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’ Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba, abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata.
4
“Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana zan tambaye ka, kuma za ka amsa mini.’
5
Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka.
6
Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.”
Settings